logo

HAUSA

Zurfafa kwaskwarima alama ce ta kasar Sin a sabon zamani

2022-12-28 10:49:11 CMG Hausa

Tun bayan da shugaban kolin kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da rahoton murnar zuwan sabuwar shekara a karo na farko, a kusan ko wace shekara ya kan ambaci kalmar “kwaskwarima” a wannan muhimmin lokaci wato tsakanin karshen shekarar da ta kare da farkon shekara mai zuwa. Ana iya cewa, kalmar “kwaskwarima” tana shafar dukkanin manufofin tafiyar da harkokin kasa na Xi Jinping.

Abun farin ciki shi ne, tun bayan da aka kira babban taron wakilan JKS karo na 18 a shekarar 2012, sai kwamitin kolin jam’iyyar dake karkashin jagorancin Xi Jinping ya cimma burikan tabbatar da manyan sauye-sauye a fannoni daban daban na kasar, har ya bude sabon shafin kwaskwarima da bude kofa ga ketare a kasar. An gani a bayyane cewa, kara zurfafa kwaskwarima a dukkan fannoni ya kasance alama ta kasar Sin a sabon zamanin da ake ciki. (Jamila)