logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Karfafa Matakan Yaki Da COVID-19 Ga Muhimman Rukunonin Jama’a Da Wurare

2022-12-27 19:52:32 CMG HAUSA

Kasar Sin ta kara daukar matakan kandagarki da dakile annobar COVID-19 a muhimman wurare, kungiyoyi da rukuninin jama'a, a daidai lokacin da kasar ta sauya matakanta na yaki da cutar COVID-19.

Muhimmiyar takardar, wadda kwamitin yaki da annobar na majalisar gudanarwar kasar ya fitar, ta lura cewa, ya kamata a kara adadin rigakafin da ake yiwa mutanen da ke zaune a wuraren kula da tsoffi da cibiyoyin jin dadin jama'a, yayin da mutane ke cikin hadarin ci gaba da shiga yanayi mai tsanani, ciki har da mutane masu shekaru 60 zuwa sama, mutanen da ke da wani rashin lafiya, da wadanda ba su da karin garkuwar jiki, aka shawarce su da su hanzarta karbar allurar dake kara karfin garkuwa. (Ibrahim)