logo

HAUSA

CMG ya yi bitar murnar bikin bazara na 2023 karo na farko

2022-12-27 10:58:46 CMG Hausa

Babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG ya yi bitar murnar bikin bazara na gargajiyar kasar Sin na shekarar 2023 mai taken “Kasar Sin mai wadata a sabon zamani da kara dadin rayuwar al’ummar Sinawa” a karo na farko a jiya Litinin, inda aka nuna kwazo da himman Sinawa masu cike da imani.

Ana ci gaba da nacewa kan manufar kirkire-kirkire yayin da ake shirya murnar bikin bazara na shekarar 2023 dake tafe, inda za a nuna halayyar jarumtaka ta al’ummar Sinawa ‘yan kabilu daban daban ta hanyar samar da shirye-shirye iri iri kamar su wake-wake, da raye-raye, da wasan kwaikwayo da sauransu.

‘Yan wasan fasaha wadanda suka halarci bitar bikin sun yi kokari matuka domin nuna wa masu kallo sabon ci gaban da kasar Sin ta samu a sabon zamanin da ake ciki. Za a yi murnar bikin bazara na shekarar 2023 a ranar 21 ga watan Janairun shekara mai zuwa wato rana ta karshe ta shekarar 2022 bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin. (Jamila)