logo

HAUSA

Dangantakar Sin Da Afrika Ta Kai Wani Mataki Da Babu Wanda Zai Iya Lalatawa

2022-12-27 17:53:07 CMG Hausa

Yayin da ake gab da adabo da shekarar 2022, jajirtattun injiniyoyin Sin da Afrika, sun himmantu badare ba rana, domin ganin kammaluwar ginin hedkwatar cibiyar kandagarki da yaki da yaduwar cututtuka ta Afrika wato Afrika CDC.

Duniya ta shaida yadda annoba a wuri kan iya yaduwa cikin kankanin lokaci har ma ta zama barazana ga duniya baki daya. Yadda irin wadannan annoba ke barkewa a Afrika, na bukatar shiri da dauki na gaggawa.

Yadda Sin ta dauki nauyin ginin hedkwatar cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta Afrika, gagarumar gudunmawa ce da za ta taimaka wajen kyautata lafiyar al’ummar nahiyar, inda za su shafe lokaci mai tsawo suna cin moriyarsa. Haka kuma, ya sake nuna cewa a ko da yaushe, Sin tana tare da al’ummar Afrika, kuma a shirye take ta share musu hawaye.  

Bayan taron ministocin kungiyar FOCAC a shekarar 2018 ne kasar Sin ta bayyana aniyarta ta daukar nauyin ginin hedkwatar cibiyar Africa CDC, tare da sanya dukkan kayayyakin da ake bukata a ciki. 

A watan Yulin 2020 ne kuma aka rattaba hannu kan yarjejeniyar ginin. Zuwan aski gaban goshi, ya shaida mana cewa kasar Sin na gudanar da wannan aiki ne yayin da take fama da aikin yaki da cutar COVID-19 a gida da kuma yanayi na rashin tabbas da ake fama da shi a duniya. Wato duk da wadannan kalubale, ba ta yi kasa a gwiwa ko dakatar da aikin ba, sai ma dukufa da ta yi don ganin an kammala shi kamar yadda aka tsara. 

Hakika kasar Sin ta amsa sunanta na babbar kasa kuma babbar yaya, wadda ke burin ganin ci gaban ’yan uwanta kasashe masu tasowa, inda a ko da yaushe, take nacewa wajen aiwatar da ayyuka na gani na fada, masu amfani da al’ummar Afrika ke matukar bukata. Wannan ya kai dangantakar sassan biyu wani matsayi da ba za a iya lalatawa ba. 

Mun riga mun san cewa, annoba ba ta san iyakar kasa ko jinsi ba, don haka, tana iya bulla a ko ina. Sai dai, yadda aka shiryawa tunkararta zai ba da damar cin galaba a kanta. Taimakon kasar Sin na ginin hedkwatar da samar da kayayyaki a cikinsa, zai karawa nahiyar Afrika karfin tunkara da yaki da duk wata annoba da ka iya bullowa nan gaba, lamarin da zai rage asarar rayuka da ma dogaro da kasashen waje ta fuskar samar da magunguna ko riga kafi ba, domin mun ga yadda kasashe dake kiran kansu manya, suka yi ta boye alluran riga kafin COVID-19 domin amfanin kansu ba tare da tunawa da wadanda ba su da karfi ba. Haka zalika, wannan cibiya na iya zama wani dandali da kwararrun Sinawa za su taimaka wajen bunkasa kwarewar takwarorinsu na Afrika. (Fa’iza Mustapha)