logo

HAUSA

Kasar Sin ta dage ka’idojin yaki da COVID-19 ga matafiya daga ketare

2022-12-27 14:44:07 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar a yau Talata cewa, daga ranar 8 ga watan Junairu, za a soke gwajin cutar COVID-19 ga matafiyan daga ketare.

Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen ta wallafa a shafinta na yanar gizo, ta ce ana shawartar masu zuwa kasar Sin daga ketare, su yi gwajin cutar sa’o’i 48 kafin lokacin tafiyarsu. Inda kuma ake shawartar wadanda gwaji ya nuna sun kamu da cutar, su jinkirta tafiyar zuwa lokacin da gwaji zai nuna ba sa dauke da ita.

Haka kuma, babu bukatar matafiya su nemi manhajar tantance yanayin cutar ta Health Code, daga ofisoshin jakadancin kasar Sin.

A cewar sanarwar, za su bayyana yanayin lafiyarsu ne a katin da za su gabatarwa jami’an kwastam. Wadanda kuma yanayin lafiyarsu ke da matsala ko suke dauke da zazzabi, za su yi gwaji a wurin, sannan kuma za a nemi su killace kansu a gida ko su je asibiti, bisa la’akari da yanayin lafiyarsu. (Fa’iza Mustapha)