Kasar Sin za ta sassauta dabarunta na yaki da cutar COVID-19
2022-12-27 11:30:57 CMG Hausa
A kokarinta na sauya manufofinta kan cutar COVID-19, kasar Sin ta sauya matakan yaki da cutar daga rukunin A zuwa rukunin B.
Wata sanarwa da hukumar kula da lafiya ta kasar ta fitar jiya Litinin, ta ce kasar Sin ta kuma sauyawa cutar suna daga "novel coronavirus pneumonia" wato matakin cutar mai tsanani dake shafar huhu, zuwa "novel coronavirus infection”.
Haka kuma, daga ranar 8 ga watan Junairu na shekarar 2023 dake tafe, kasar Sin za ta sassauta matakanta na yaki da cutar daga rukunin A zuwa rukunin B, bisa dokokin kandagarki da yaki da cutar, tare da cire ta daga jerin cututtukan dake bukatar killacewa, bisa dokokin kiwon lafiya da na killacewa na kasar.
Yanzu haka, an mayar da cutar COVID-19 zuwa rukunin B, amma kuma matakan kandagarki da dakile yaduwarta na karkashin rukunin A.
Sawarwar da kwamitin kula da matakan kandagarki da dakile yaduwar cutar, na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar a jiyan, ta ce an riga an dauki dukkan matakan da suka kamata, wadanda za su taimakwa wajen daidaita sassauta matakan, bisa dogaro da yanayin sauyawar cutar da kuma yadda ake tunkararta a kasar. (Fa’iza Mustapha)