Tsananin hunturu da aka fuskanta a kasar Amurka
2022-12-27 20:27:32 CMG Hausa
Labarin da kafar NBC ta bayar ya yi nuni da cewa, ya zuwa ranar 25 ga wata, tsananin hunturu da aka fuskanta a kasar Amurka ya riga ya halaka mutane a kalla 35. A birnin Buffalo na jihar New York da ma sassan da ke kewayensa, bala’in ya halaka mutane a kalla 7, kuma gwamnar jihar Kathy Hochul ta yi kira ga mazauna jihar da su yi kokarin kauracewa fita daga gida.(Lubabatu)