logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Dage Ka’idojin Yaki Da Annobar COVID-19 Ga Matafiya Daga Ketare

2022-12-27 20:14:33 CMG HAUSA

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar a yau Talata cewa, daga ranar 8 ga watan Janairun shekarar 2023, za a soke gwajin annobar cutar COVID-19 ga matafiyan daga ketare.

Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta wallafa a shafinta na yanar gizo, ta ce ana shawartar masu zuwa kasar Sin daga ketare, su yi gwajin cutar sa’o’i 48 kafin lokacin tafiyarsu. Inda kuma ake shawartar wadanda gwaji ya nuna sun kamu da cutar, su jinkirta tafiyar zuwa lokacin da gwaji zai nuna ba sa dauke da ita.

Haka kuma, babu bukatar matafiya su nemi manhajar tantance yanayin cutar ta Health Code, daga ofisoshin jakadancin kasar Sin.

A cewar sanarwar, za su bayyana yanayin lafiyarsu ne a katin da za su gabatarwa jami’an kwastam. Wadanda kuma yanayin lafiyarsu ke da matsala ko suke dauke da zazzabi, za su yi gwaji a wurin, sannan kuma za a nemi su killace kansu a gida ko su je asibiti, bisa la’akari da yanayin lafiyarsu.

A cewar sanarwar, kasar Sin za ta soke matakan takaitawa da ta sanya wa jiragen saman fasinja na kasa da kasa, inda za ta kara yawan zirga-zirgar jiragen sama bisa matakai, da inganta hanyoyin da jiragen ke bi.

Bugu da kari, kamfanonin jiragen sama za su ci gaba da fesa maganin kashe kwayoyin cuta a cikin jiragensu, kuma ana bukatar fasinjoji su sanya abin rufe fuska da baki yayin da suke cikin jirgi.

Kasar Sin za ta kara inganta tsare-tsare ga baki da ke shigowa kasar Sin don yin aiki, kasuwanci, karatu, ziyara da haduwa da dangi, da samun viza cikin sauki yadda ya kamata.

Sanarwar ta bayyana cewa, za a dauki matakan tabbatar da cewa, jigilar kayayyaki a tashoshin jiragen ruwa daban-daban, za su koma kamar yadda suke kafin barkewar cutar, kuma za a dawo da harkokin yawon bude ido ga 'yan kasar Sin cikin tsari.

Wadannan sauye-sauye, sun yi daidai da ingantattun matakan rigakafin kamuwa da cutar a cikin gida, za kuma su daidaita matakan rigakafin annobar da sarrafawa tare da ci gaban tattalin arziki da zamantakewa da kuma sanya tafiye-tafiye tsakanin kasashe kan turba mafi dacewa, aminci, tsari da inganci.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Wang Wenbin ya yi wadannan kalamai ne, a yayin taron manema labarai da aka saba shiryawa, Talatar nan, lokacin da aka tambaye shi game da sabbin matakan. (Fa’iza&Ibrahim)