Hadarin mota ya hallaka mutane 6 a jihar Bauchi dake arewacin Najeriya
2022-12-26 11:36:24 CMG Hausa
Rundunar kare hadurra ta Najeriya, ta ce wani hadarin mota da ya auku a jiya Lahadi a yankin Ganjuwa na jihar Bauchi dake arewa maso gabashin kasar ya hallaka mutane 6, tare da jikkata wasu mutane 16, sakamakon fashewar taya da ta sanya wata mota dauke da fasinjoji faduwa.
Da yake tabbatar da aukuwar hadarin yayin wani taron manema labarai, kakakin rundunar reshen jihar Bauchi Yusuf Abdullahi, ya ce cikin wadanda hadarin ya ratsu da su 6 sun rasu nan take, yayin da aka garzaya da wadanda suka ji raunuka zuwa asibiti, domin samun kulawar jami’an lafiya. (Saminu Alhassan)