logo

HAUSA

Zimbabwe Da Sin Sun Sabunta Yarjejeniyar Tusa Keyar Masu Aikata Laifi

2022-12-25 14:33:12 CMG HAUSA

Ministan harkokin cikin gida da al'adun gargajiya na kasar Zimbabwe Kazembe Kazembe ya bayyana cewa, kasashen Zimbabwe da Sin, sun sabunta yarjejeniyar da suka cimma game da mika masu aikata laifi ga juna daga ranar 23 ga watan Disamban shekarar 2022.

Kasashen biyu sun fara sanya hannu kan yarjejeniyar ce a shekarar 2018. A karkashin yarjejeniyar, dukkan kasashen 2 sun dauki alkawarin mika wa 'yar uwarta wadanda aka samu a yankinta da daya kasar ke, domin gurfanar da su a gaban kuliya bisa zargin aikata laifin da ya saba wa kasashen biyu, ko kuma su yi zaman kaso idan har an yanke musu hukunci, kamar yadda jaridar Herald ta bayar da rahoto.

Duk da haka, babu wata kasa da za ta mika 'yan kasarta, amma idan har hakan ya faru, za ta dauki nauyin gudanar da shari'a a karkashin dokarta.(Ibrahim)