Xi Jinping ya amsa wasikar masu fasaha na kamfanin wasannin fasaha na kasar Sin
2022-12-25 21:56:31 CMG Hausa
A jiya ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa wasikar da masu fasaha daga kamfanin wasannin fasaha na kasar Sin suka rubuta masa, inda ya yi nuni da cewa, a cikin wadannan shekaru, masu fasahar sun gabatar da shirye-shirye da dama masu kyau, wadanda suka samar da muhimmiyar gudummawa kan raya adabi da fasaha, da yin musayar al’adu da kasashen waje, sun kasance wakilan kasar Sin ta fuskar al’adu. Shugaba Xi yana fatan za su ci gaba da samar da sabuwar gudummawa wajen raya kasa mai tsarin gurguzu a fannin al’adu. (Zainab Zhang)