MDD: kananan yara miliyan 25 sun rasa damar a yi musu allurar tilas a shekarar 2021 a baki dayan duniya
2022-12-25 15:16:53 CMG HAUSA
MDD ta kaddamar da rahoto a kwanan baya cewa, sakamakon yaduwar annobar cutar COVID-19, da kawo tsaiko ga tsarin samar da kayayyaki a duniya, da karuwar bayanan karya, ya sa kananan yara kimanin miliyan 25 sun rasa damar samun allurar rigakafin tilas a duk duniya a shekarar 2021, adadin da ya kafa tarihi a cikin shekaru misalin 30 da suka wuce.
Hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa WHO da Asusun kula da kananan yara na MDD sun fito da rahoton bisa bayanai daga tsarin lafiya na kasashe da yankuna 177. Rahoton ya ce, a shekarar 2021, yawan kananan yara da aka yi musu allurar rigakafin tarin jirirai, makarau da rinku duka ya kai kaso 81, wanda ya ragu da kaso 5 bisa na shekarar 2019, kuma adadin ya kai kaso 83 a shekarar 2020, wato kananan yara kimanin miliyan 25 a duniya sun rasa damar samun allura a kalla 1 ta rigakafin cututtuka 3 da muka ambata a baya, yawansu ya karu da miliyan 2 bisa na shekarar 2020, da kuma miliyan 6 bisa na shekarar 2019. Ban da haka kuma, kananan yara miliyan 24.7 sun rasa damar samun allura ta farko ta rigakafin kyanda a duniya, wasu miliyan 14.7 sun rasa damar a yi musu allurar ta biyu, ta haka yawan wadanda aka yi musu allurar rigakafin kyanda ya ragu zuwa kaso 81, adadin da ya fi kankanta tun bayan shekarar 2008.
Karuwar yawan kananan yara da suka rasa damar samun allurar rigakafin tilas, ta haifar da karuwar barazanar da karin kananan yara ka iya fuskanta wajen kamuwa da wasu cututtukan musamman, wadanda da ma akan iya kandagarkinsu ta hanyar allurar.
Alkaluma sun nuna cewa, a shekarar 2021, kananan yara kimanin miliyan 18 a duniya ba a yi musu allurar rigakafin tarin jirirai, makarau da rinku 3 duka ba, wadanda yawancinsu suka fito ne daga kasashen Habasha, Indiya, Indonesia, Nijeriya, Philippines da wasu kasashe masu tasowa. Adadin ya kai miliyan 13 kawai a shekarar 2019.
Rahoton ya yi bayani da cewa, akwai dalilai da dama da suka haifar da karuwar yawan kananan yara da ba a yi musu allurar rigakafin tilas a duniya a shekarar 2021 ba, baya ga yaduwar annobar cutar ta COVID-19, karuwar yawan kananan yara da suke zaune a yankunan da rikici ya shafa, wani muhimmin dalili ne na daban.
Rahoton ya yi kira ga kasashen duniya da su karfafa gwiwar yin allurar rigakafi. Kamar yadda hukumar WHO ta bayyana, yayin da muke yaki da annobar cutar COVID-19, tilas ne mu mai da hankali kan yin allurar rigakafin cututtukan kyanda, ciwon huhu, zawayi, da sauran cututtuka masu kisa. (Tasallah Yuan)