logo

HAUSA

Sin ta kalubalanci Amurka da ta gyara kuskurenta kan batun tambarin Hong Kong

2022-12-23 12:57:40 CMG Hausa

A ranar 21 ga wata ne, kwamitin kwararru na WTO wanda ke daidaita takkadamar dake tsakanin yankin Hongkong na kasar Sin da Amurka kan batun inda ake samar da kayayyaki na asali, ya yanke hukunci cewa, matakan da kasar Amurka ta dauka kan yadda ake alamta asalin inda ake samar da kayayyaki sun saba wa ka'idojin WTO. Game da wannan hukunci, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a jiya cewa, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta mutunta hukuncin kwamitin kwararrun tare da daukar kwararan matakai don gyara kuskuren da ta yi.

Mao Ning ta bayyana cewa, kasar Amurka tana fakewa da batun tsaron kasa kan kasa da kasa ko yankuna, da siyasantar da batutuwan cinikayya, hakan ya sabawa ka’idojin hukumar WTO, kana ba su dace da moriyarta ba. Don haka, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta mutunta hukuncin kwamitin, da daukar matakai don gyara kuskurenta, da kiyaye tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban daban na WTO, da kiyaye tsarin cinikayya na duniya yadda ya kamata. (Zainab Zhang)