Shugaba Xi ya gana da manyan jami’an gudanarwar yankunan musamman na Hong Kong da Macao
2022-12-23 21:30:27 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da babban jami’in gudanarwar yankin musamman na Hong Kong John Lee, wanda ke ziyarar aiki a Beijing.
Lokacin ganawar tasu a yau Juma’a a birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin, shugaba Xi ya saurari rahoto daga Lee, dangane da yanayin da yankin Hong Kong ke ciki, da kuma ayyukan hukumar yankin.
Har ila yau a dai yau din, shugaba Xi ya zanta da babban jami’in gudanarwar yankin musamman na Macao Ho Iat Seng, wanda shi ma ke ziyarar aiki a birnin Beijing.
Yayin zantawar tasu shugaba Xi ya saurari halin da yankin na Macao ke ciki da ma rahoton ayyukan hukuma daga Mr. Ho. (Saminu Alhassan)