logo

HAUSA

Wang Yi: Ya kamata Sin da Amurka su yi aiki tare don magance kalubalen da duniya ke fuskanta

2022-12-23 10:57:17 CMG Hausa

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya bayyana cewa, ya kamata kasashen Sin da Amurka su yi aiki tare, domin tunkarar kalubalen da duniya ke fuskanta. 

Wang ya yi wannan kira ga Washington ne jiya Alhamis a birnin Beijing, yayin ganawa da daya daga shugabannin kungiyar kasa da kasa ta kasashen Asiya John Thornton, wata kungiya mai zaman kanta da ke birnin New York, dake bunkasa makomar bai daya ta kasashen Asiya da duniya baki daya a fannin siyasa da sauransu. 

Wang ya kara da cewa, a yayin da ake fuskantar karuwar batutuwa masu sarkakiya da suka shafi yankin da kuma kalubalen da duniya ke fuskanta, kamar sauyin yanayi da matsalar abinci da makamashi, ya dace kasashen Sin da Amurka a matsayinsu na manyan kasashe biyu wadanda ke sauke nauyin dake bisa wuyansu, su aiwatar da hadin gwiwar da ta dace, kamar yadda al’ummar duniya ke fatan hakan. 

A nasa bangaren, Thornton ya bayyana cewa, ya kamata Amurka da Sin su kasance abokan huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, wadanda za su iya yin aiki tare. Yana mai cewa, a shirye yake ya ci gaba da taka rawa wajen inganta mu'amalar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Amurka da Sin, da kara fahimtar jama'ar Amurka game da kasar Sin, da sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar dake tsakanin Amurka da Sin.

Ya ce, ya kamata Amurka ta kalli kasar Sin yadda take, ta daina neman dakile ta da mayar da ita saniyar ware ba tare da wata hujja ba, sannan ta koma kan kyakkyawar manufa mai inganci game da kasar Sin. (Ibrahim Yaya)