logo

HAUSA

Babban bankin Sin ya lashi takobin aiwatar manufofin kudi bisa yanayi mafi dacewa

2022-12-22 11:27:49 CMG Hausa

 

Babban bankin kasar Sin ya yi alkawarin aiwatar da manufofin kudi bisa yanayi mai karfi da dacewa.

A cewar babban bankin, zai yi kokarin ganin yanayin sayar da kadarori a tsarin hada hadar kudi ya samu wadatattun manufofin kudi kamar na saye da sayar da hannayen jari daga bankin.

Bankin zai kuma taimakawa bangarori kamar na kayayyakin masarufi da aiwatar da muhimman ababen more rayuwa da wasu manyan ayyuka, tare da taimakawa kananan harkokin kasuwanci masu zaman kansu.

Domin tabbatar da hada-hadar kudi na gudana cikin aminci, bankin zai mayar da hankali wajen shawo kan hadduran da suka shafi bangaren dillancin gidaje da dandalin kasuwanci da kuma muhimman harkokin kasuwanci da kanana da matsakaitan cibiyoyin kudi.

Haka kuma, bankin ya nanata cewa, zai sakarwa manufofi mara su taka rawar da ta kamata da karfafawa cibiyoyin hada-hadar kudi gwiwar kara bayar da rance, ta yadda zai taimaka wajen daidaita samun ci gaba da samar da ayyukan yi da farashin kayayyaki, da kuma tabbatar da tattalin arzikin kasar na ci gaba bisa matakin da ya dace.(Fa’iza)