Wang Yi ya yi tattaunawa tare da takwarar aikinsa ta kasar Australia Penny Wong
2022-12-22 12:56:09 CMG Hausa
Memban hukumar siyasa ta kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya yi tattaunawa kan harkokin waje da manufofi, tsakanin Sin da Australia zagaye na 6 tare da ministar harkokin wajen kasar Australia Penny Wong a nan birnin Beijing.
Wang Yi ya bayyana cewa, Penny Wong ta kawo ziyarar a yayin da aka cika shekaru 50 da Sin da Australia suka sa hannu kan sanarwar kulla dangantakar diplomasiyya, wadda take da babbar ma’ana. Ya ce ya kamata bangarorin biyu su aiwatar da ayyukan da shugaban kasar Sin Xi Jinping da firaministan kasar Australia Anthony Albanese suka cimma daidaito kan su, a yayin da suka yi ganawa a tsibirin Bali na Indonesiya, da kiyaye girmama juna, da amincewa da bambance-bambance a tsakaninsu, da hadin gwiwa, da samun moriyar juna don sa kaimi ga kyautata dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a dogon lokaci yadda ya kamata.
A nata bangare, Penny Wong ta bayyana cewa, dangantakar dake tsakanin Australia da Sin mai aminci, ta dace da moriyar kasashen biyu da yankinsu. Kuma sabuwar gwamnatin kasar Australia ta tsaya tsayin daka kan manufar Sin daya tak, da daidaita matsalolin dake kasancewa a tsakanin kasashen biyu, da bunkasa hadin gwiwarsu a fannoni daban daban bisa tsarin raya dangantakar abota a tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni.
Bayan shawarwarin, bangarorin biyu sun gabatar da wata hadaddiyar sanarwa kan sakamakon shawarwarin. (Zainab Zhang)