logo

HAUSA

Shin kasar Amurka za ta iya cika alkawarinta?

2022-12-20 10:37:49 CMG Hausa

Kwanan baya, kasar Amurka ta kira taro karo na 2 na shugabanninta da na kasashen Afirka, shekaru 8 bayan shirya taron a karon farko.

Idan aka kalli tsarin taron, za a ce wani gagarumin biki ne, wanda ya samu halartar shugabannin kasashe 49 dake nahiyar Afirka, da na kungiyar tarayyar Afirka AU, gami da takwarorinsu na kasar Amurka. A cewar fadar White House, ta wannan taro, kasar Amurka ta kuduri aniyyar zurfafa huldarta da nahiyar Afirka, kana gwamnatin kasar karkashin jagorancin shugaba Joe Biden ta sanar da shirin zuba jari na dala biliyan 55 ga kasashen Afirka, cikin shekaru 3 masu zuwa.

Duk da haka, ba a rasa ce-ce-ku-ce game da taron. Misali, tsohuwar jakadiyar kungiyar AU a kasar Amurka , Arikana Chihombori-Quao, ta ce taron ba zai haifar da da mai ido ba, illa dai Amurkawa su ci gaba da nuna bambanci ga jama’ar nahiyar Afirka.

Hakika kasashen Afirka na da dimbin al’umma da albarkatun kasa, inda tattalin arzikinsu ke sauyawa daga na salon gargajiya zuwa irin na zamani, don haka suna bukatar samun karin jari daga kasashen ketare, wanda zai iya taimakawa kokarinsu na raya kasa. Sai dai a ganin wasu masana masu nazarin al’amuran kasa da kasa, dalilin da ya sa kasar Amurka ke son kara zuba jari a nahiyar Afirka, shi ne domin neman biyan bukatarta ta samun fifiko yayin takara da sauran kasashe.

Abun da kasashen Afirka suke bukata, shi ne taimakon da aka bayar bisa sahihanci. Idan kasar Amurka na son daidaita huldarta da kasashen Afirka, to, ya kamata ta girmama kasashen Afirka, da samar musu da hakikanan abubuwa masu amfani da suke bukata, yayin da suke kokarin raya tattalin arzikinsu. (Bello Wang)