logo

HAUSA

‘Yan bindiga sun kashe mutane da dama a arewacin Najeriya

2022-12-20 11:11:48 CMG HAUSA

 

Wasu majiyoyi daga Najeriya na cewa, an kashe mutane da dama a wasu hare-hare da wasu ‘yan bindiga suka kai kan wasu kauyuka biyu a jihar Kaduna da ke arewacin kasar,

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya bayyana a wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafi cewa, hare-haren da aka kai a daren ranar Lahadin da ta gabata, sun shafi kauyukan Malagum 1 da Sokwong da ke karamar hukumar Kaura a jihar ta Kaduna, inda ‘yan bindigar suka kona gidaje da sauran kadarori,

Aruwan ya ce, sojoji da sauran jami’an tsaro, sun kai rahoton abubuwan da suka faru a kudancin Kaduna ga gwamnatin jihar. Sai dai jami'in bai bayyana hakikanin adadin wadanda suka mutu a cikin sanarwar lokacin da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya tuntube shi. Sai dai ya ce, jami’an tsaro na ci gaba da kaiwa yankin daukin gaggawa, da nufin cafke bata garin.(Ibrahim)