logo

HAUSA

Sinawa suna tinkarar COVID-19 da karfin gwiwa

2022-12-20 16:46:48 CMG Hausa

Wasu abokai sun rubuta mana sakonni a kwanan baya, inda suka tambaye ni kan yanayin da ake ciki a nan kasar Sin, a fannin tinkarar cutar COVID-19. Amsa ita ce, wata sabuwar barkewar cutar nau’in Omicron ta haifar da wasu matsaloli, sai dai ba ta girgiza karfin gwiwar Sinawa ba.

A yayin barkewar nau’in Omicron ta wannan karo, birnin Beijing, inda nake zaune, yana daga cikin wuraren da suka fi fama da yaduwar annobar. Wasu makwabta da abokaina da yawa sun kamu da ita, inda suka fara zazzabi da tari. Ko da yake galibin mutanen da suka kamu da cutar, alamun da suka nuna ba su da tsanani. Amma saboda dimbin mutanen da suka kamu da cutar ake samu a lokaci guda, ya sa an samu cukuson mutane a asibitoci, da karancin wasu magunguna a shagunan sayar da magani.

Ban da wannan kuma, don magance yin cudanya da mutane masu dauke da kwayoyin cutar COVID-19, jama’a sun daina zuwa sayen kayayyakin abinci da na masarufi a kasuwanni, maimakon haka, sun karkata ga shafukan sayar da kayayyaki na yanar gizo ta Internet gaba daya, lamarin da ya sa ake fuskantar matsalar karancin ma’aikatan jigilar kaya. Don haka yanzu a kan jira karin wasu kwanaki, kafin a iya samun kayan da aka saya ko oda.

To, wadannan su ne matsalolin da ake fuskanta a halin yanzu. Sai dai Sinawa ba su damu sosai ba, ganin yadda suka fara daukar wasu matakai don tinakarar matsalolin. Misali, an bude wuraren ganin likita na wucin gadi, don biyan bukatar mutanen da suke neman ganin likita. Kana an kayyade yawan magunguna da za a iya saya a lokaci guda, ta yadda kowa zai iya samun maganin da yake bukata cikin gaggawa. Ban da wannan kuma, an tura karin ma’aikatan jigilar kayayyaki zuwa wuraren da suka fi fama da annoba, da sanya galibin mutane yin aiki daga gida don magance duk wata kafa ta yaduwar cuta, da lallashin mutane don su huta a gida maimakon zuwa asibiti, idan alamunsu ba su da tsanani.

To, tambaya ita ce, me ya sa Sinawa basa damuwa, ko da yake cutar COVID-19 na yaduwa cikin sauri?

Saboda sun san matsalar ba za ta dade ba, musamman ma a fannin tattalin arziki. Cikin shekaru 3 da suka wuce, kasar Sin ta yi kokarin daukar tsauraran matakai na hana yaduwar cutar COVID-19, kamar takaita zirga-zirga, da umartar ‘yan kasa don yin gwaji, da killace wadanda suka kamu da cutar har zuwa lokacin da suka warke, da dai sauransu, don kare lafiyar jama’ar kasar, ko da yake matakan na haifar da matsi a fannin tattalin arizki. Amma duk da haka, matakan ba su hana ci gaban tattalin arzikin kasar Sin ba, inda matsakaiciyar karuwar GDPn kasar cikin wadannan shekaru 3 ta kai kashi 4.6%, gaba da na sauran manyan kasashe irinsu Amurka, da Japan, da Jamus, da Faransa. Sa’an nan zuwa wannan lokacin da muke ciki, kasar Sin ta daidaita manufarta ta kandagarkin yaduwar cuta, inda ta sassauta wasu matakan kayyadewa, bisa la’akari da sabon yanayin da aikin tinkarar cutar ke ciki. Hakan ya sa ‘yan kasar ke sa ran ganin karuwar tattalin arizkin Sin cikin karin sauri, bayan da yanayin bazuwar nau’in Omicron na cutar na wannan karo ya kai karshe.

Sa’an nan, wani dalili na daban da ya kawar da damuwar Sinawa, shi ne amincewarsu kan gwamnatin kasar. Sun fahimci dabarar gwamnatin a fannin tsara manufofi: Ta kan tsara wata manufa bisa hakikanin yanayin da kasar ke ciki, da kokarin daidaita manufar a kai a kai, bisa sauyawar sharadi. Ganin yadda kasar Sin ke da tsoffin da yawansu ya kai fiye da kashi 17% na yawan al’ummarta, wadanda kuma suka fi fuskantar hadari idan sun kamu da cutar COVID-19, ya sa kasar daukar tsauraran matakai na dakile cutar cikin shekaru 3 da suka wuce. Sa’an nan zuwa yanzu, yadda fiye da kashi 91% na tsoffin kasar suka riga suka karbi allurar rigakafin cutar, da yadda karfin yaduwar cutar nau’in Omicron ke karuwa, amma kuma karfinta na haddasa mutuwa ke raguwa, sun sa gwamnatin kasar Sin samun damar daidaita manufarta ta kandagarkin cutar.

Duk wata manufa da aka dauka a kasar Sin, jama’ar kasar na da cikakken karfin gwiwa kan cewar, gwamnati za ta kare moriyar daukacin al’ummar kasar, bisa akidarta ta kokarin bautawa jama’a. (Bello Wang)