logo

HAUSA

Dakarun sojin saman Najeriya sun kubutar da wasu ’yan kasar Sin 7 daga hannun masu garkuwa da mutane

2022-12-20 10:37:42 CMG Hausa

A ranar Lahadi 19 ga wata rundunar musamman ta dakarun sojin saman Najeriya sashe na 271 ta yi nasarar ceto wasu ’yan kasar Sin 7 daga hannun masu garkuwa da mutane a dajin Birnin Gwari dake jihar Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya.

Dakarun sun yi musayar wuta kafin daga bisani su samu galaba kan ’yan ta`addan.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da cigaban rahoton.

 

Su dai wadannan ’yan kasar Sin 7 da aka samu ceto rayukansu sun bayyana cewa, suna sana`ar hakar ma`adanai ne a wasu yankuna dake karamar hukumar Shiroro a jihar Niger dake yankin arewa ta tsakiyar Najeriya.

Kuma an yi garkuwa da su din ne tun a watan shida na wannan shekara ta 2022 kamar yadda kakakin rundunar sojin sama ta Najeriya Air Kwamado Edward Gab-Kwet ya shaidawa manema labarai.

Ya ce, dakarun musamman su 35 ne suka gudanar da wannan aikin na samame, inda suka shafe daren Lahadi a yankin Kamfani Doka da Gwaska suna musayar wuta da masu garkuwa da mutanen har sai da suka fatattake su daga tsaunuka da kogunan duwatsu da suke da mafaka.

Air Kwamado Edward Gab-Kwet kakakin rundunar sojin saman na Najeriya ya ci gaba da yi min bayani kamar haka,

“Tun da ma ana mun sami labarin wadannan ’yan bindiga sun yi  garkuwa da wasu mutane, wannan ta sa muka yi shiri na musamman domin mu afka masu. Bayan mun isa daf da inda suke sai jikin su ya ba su cewa sojoji sun kawo masu hari nan da nan suka fara budewa dakarunmu wuta. Daga nan ne su ma suka fara mayar da martini, da suka ji cewa karfin dakarunmu ya zarta nasu sai suka gudu suka bar bindigogin su da mutanen da suka yi garkuwa da su. Bayan dakarun namu sun isa mafakar ’yan ta`addan shi ne sai suka tarar da ’yan kasar Sin 2 a inda suke sanar da cewa sauran Sinawa 5 din suna wani sashe na daban da ake tsare da su, sai aka je aka same su a wannan wuri, to, dukkansu guda 7 din an same su, kuma don Allah mun mayar da su sansaninmu dake Kaduna.”

Tuni dai babban hafsan sojin sama na tarayyar Najeriya Air Marshal Oladayo Amao ya jinjinawa dakarun da suka gudanar da wannan aiki a maboyar ’yan ta’addan dake Birnin Gwari a jihar ta Kaduna.

Air Marshal Oladayo ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su ci gaba da baiwa sojoji da sauran jami’an tsaro hadin kai ta wajen ba su bayana n da za su taimaka wajen kamo ’yan ta`adda a duk inda suke a kasar. (Garba Abdullahi Bagwai)