Tattalin Arzikin Kasar Sin Zai Bunkasa A Shekarar 2023
2022-12-20 11:06:32 CMG HAUSA
Yayin da ake tunanin ci gaban duniya zai yi rauni sosai a shekarar 2023, a bangare daya kuma ana sa ran tattalin arzikin kasar Sin zai farfado ya kuma inganta.
Jami’in ofishin kwamiti mai kula da harkokin kudi da tattalin arziki na kwamitin tsakiya na JKS ne ya bayyana hakan, bayan kammala taron aikin raya tattalin arzikin kasar Sin da aka gudanar a makon jiya.
Yana mai cewa, za a iya danganta hasashen da ake na samun makoma mai haske a shekara mai zuwa ga managartan matakan yaki da annobar COVID-19 da kasar ta dauka,da ingantattun manufofin ci gaban tattalin arziki, da yanayin da ake ciki a wannan shekara.
Jami'in ya ce, kyawawan matakan yaki da COVID-19 da kasar ta kyautata, za su yi tasiri mai kyau ga tattalin arzikin kasar. Yana mai hasashen samun farfadowar tattalin arzikin kasar cikin sauri a watanni 6 na farkon shekarar 2023, musamman a rubu'i na biyu.
Ya kara da cewa, kasar za ta ci gaba da amfani da manufofinta na kara bukatu da inganta tsarin a shekara mai zuwa, tare da bullo da sabbin matakan da suka dace da ainihin bukatun. (Ibrahim)