logo

HAUSA

Matakan Sin na yaki da COVID-19 sun haifar da da mai ido

2022-12-20 19:13:18 CMG Hausa

Cibiyar yada shirye-shirye da harsunan Asiya da Afrika, na Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, ya gudanar da wani taron karawa juna sani kan yanayin kasar Sin a kokarinta na dakile cutar COVID-19.

Idan ba a manta ba, kasar Sin ce kasa ta farko da ta sanar da bullar cutar a hukumance ga hukumar lafiya ta duniya a karshen shekarar 2019, duk da cewa, sakamakon tarin bincike sun nuna cewa, an samu bullar cutar a wurare da dama kafin a same ta a kasar Sin. Baya ga haka, har kawo yanzu, babu wata kasa da ta taka rawar gani wajen yaki da cutar kamar kasar ta Sin.

Wasu kafafen yada labarai na yammacin duniya da ma gwamnatocinsu, sun yi ta yada jita-jitar cewa, matakan kasar Sin sun take hakkokin bil adama. Sai dai akasin abun da suke nufi, matakan kasar Sin sun cancanci jinjina matuka, domin sun taka rawar gani wajen kare al’umma daga rasa rayukansu sanadiyyar kamuwa da cutar, haka kuma sun kare yaduwar cutar daga kasar zuwa sauran sassan duniya. Gani ya kori ji, domin duk wani dake kasar Sin zai bada shaidar cewa, matakan sun taka rawar gani. Idan kuma aka duba su kasashen masu yada jita jitar, har yanzu ba su kama kafar Sin wajen yaki da cutar ba, haka kuma suna fama da matsalolin tattalin arziki.

Yadda CMG ya shirya wannan taro, hakika zai kara wayar da kan al’ummomin  Afrika kan illolin dake tattare da annobar da ma yadda za su kare kawunansu, da kuma dalilan Sin din na daukar matakan da ta dauka, tare da wayar musu da kai daga karai-rayi ko jita-jita da aka yi ta yadawa dangane da su. Baya ga haka, zai zama darasi ta yadda gwamnatocin kasashen za su iya shiryawa tunkarar annoba da mai yuwuwa ka iya barkewa a nan gaba.

Duk da cewa, ana ganin Sin ta dauki tsauraran matakai, matakan nata sun haifar da da-mai-ido, ta cimma dimbin nasarori, domin ita ce kasa daya tilo da ta samu ci gaban tattalin arziki bayan bullar annobar, haka kuma ita ce ta bayar da gudunmawa ga ci gaban tattalin arzikin duniya.

Haka zalika, wadannan kyawawan manufofi ne ya sa ake ganin yayin da ci gaban kasashen duniya zai gamu da cikas a shekarar 2023, an yi hasashen tattalin arzikin kasar Sin zai farfado tare da kara kuzari. Ingantattun manufofin kudi da Sin ta dauka da kuma saukaka matakan yaki da annobar da ta yi a baya-bayan nan, za su taimaka wajen samun habakar tattalin arzikinta wanda zai ci gaba da bayar da gudunmawa ga tattalin arzikin duniya baki daya. Haka kuma, zai kara bunkasa harkokin cinikayya da mu’amala da ma musaya da kasashe masu tasowa aminanta, musammam ma na Afrika. (Fa’iza Mustapha)