logo

HAUSA

Bunkasar tattalin arzikin zamani na kasar Sin ya samar da sabbin damammaki ga duniya

2022-12-19 13:54:51 CMG Hausa

Alkaluman kididdiga da aka fitar na nuna cewa, daga shekarar 2012 zuwa shekarar 2021, yawan tattalin arzikin zamani na Sin ya karu daga yuan triliyan 11 zuwa fiye da yuan triliyan 45, inda adadin tattalin arzikin zamani a GDP ya karu zuwa kashi 39.8% daga 21.6%.

Ya zuwa ga watan Yuni na bana, masana’antun yanar gizo, sun shafi manyan nau’o’in tattalin azrikin al’umma guda 45, inda aka saki makamashin motsi na masana'antun zamani.

A shekarar 2020, Sin ta fitar da ajandar tsaron kididdigar kasa da kasa, inda take fatan yin amfani da wannan mataki a matsayin wata madogarar tattaunawa tare da kasashen duniya, wajen tsara dokokin tafiyar da tattalin arzikin zamani na kasa da kasa dake martaba muradu bangarorin daban daban.

Bisa la’akari da gaskiyar cewa, har yanzu akwai mutane kusan biliyan 3 a duniya da ba su samu damar shiga yanar gizo ba kuma galibinsu daga kasashe masu tasowa, Sin tana sa ran yin hadin gwiwa tare da ragowar kasashen duniya, wajen tsara yanayin ci gaban tattalin arzikin zamani mai salon bude kofa da adalci, don tallafawa mutane masu karamin karfi amfana da ci gaban zamani, tare da habaka tattalin arzikin zamani, da amfanar da jama’a a fadin duniya. (Safiyah Ma)