logo

HAUSA

Cutar kwalara ta barke a kudancin kasar Nijeriya

2022-12-19 12:01:34 CMG Hausa

Rahotanni daga Nijeriya na cewa, an samu barkewar cutar kwalara a jihar Cross River dake kudancin kasar, inda ya zuwa yanzu cutar ta haddasa mutuwar mutane a kalla 20.

A cewar jami’an yankin, ya zuwa yanzu, an kwantar da mutane fiye da 30 da suka kamu da cutar. Gwamnatin ta riga tura ma’aikata da kayan aiki zuwa kauyuka da cutar ta shata, don hana cutar ci gaba da yaduwa. (Safiyah Ma)