logo

HAUSA

Australiya: an fitar da wani tsarin hasashen barazanar gamuwa da matsalar kiba da kananan yara ka iya fuskanta

2022-12-19 09:21:18 CMG HAUSA

Masu nazari da suka fito daga jami’ar Queensland sun fito da wani tsarin hasashen barazanar gamuwa da matsalar kiba da jarirai ka iya fuskanta yayin da suke lokacin yarantaka. Sun kaddamar da sakamakon nazarinsu a mujallar ilmin cututtukan kananan yara da lafiyarsu, wadda aka wallafa a Australiya a kwanan baya.

Masu nazarin sun yi bayani da cewa, sun yi nazari kan sauye-sauyen nauyin jikin jarirai cikin shekara daya bayan haihuwarsu, yadda suke barci, nauyin jikin iyayensu mata da tsayinsu kafin su samu ciki, nauyin jikin iyayensu maza da tsayinsu, ko an haife su kafin lokacin da aka tsara, ko iyayensu mata sun sha taba yayin da suke da ciki, da dai sauransu, a karshe sun fito da wani tsari wanda zai yi hasashen barazanar gamuwa da matsalar kiba da jarirai ka iya fuskanta yayin da shekarunsu suka kai 8 zuwa 9 da haihuwa.

Rahoton nazarin ya nuna cewa, an tabbatar da ingancin wannan tsari, bisa bayanan da aka tattara a baya dangane da lafiyar kananan yara kusan dubu 2 a jihar yammacin Australiya daga haihuwarsu zuwa shekarunsu su kai 9 a duniya. Ingancin hasashen da tsarin yake iya yi ya kai kaso 74.6.

Dangane da wannan tsarin hasashen barazanar gamuwa da matsalar kiba da kananan yara ka iya fuskanta, madam Zhang Chuji, likita da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani da cewa, bambanta jarirai wadanda suke fuskantar babbar barazanar samun kiba a lokacin yarantaka, yana taimakawa iyalansu daukar matakan yin rigakafi masu dacewa tun da wuri. Bayan da kananan yaran suka zama baligai, mai yiwuwa matsalar kiba za ta ci gaba da addabarsu.

Masu nazarin na kasar Australiya sun yi bayani da cewa, za su ci gaba da tababtar da ingancin tsarin a nan gaba. Idan za a sake tabbatar da ingancin tsarin, to, za a fara aiki da tsarin cikin hanzari, a kokarin taimakawa kare kananan yara gamuwa da matsalar kiba. (Tasallah Yuan)