logo

HAUSA

An sake zaben shugaba Cyril Ramaphosa a matsayin jagoran jam’iyyar ANC

2022-12-19 20:20:51 CMG Hausa

An sake zaben shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa, a matsayin shugaban jam’iyyar ANC mai mulkin kasar, yayin babban taron jam’iyyar na 55.

Shugaba Ramaphosa ya kayar da abokin takararsa Zweli Mkhize da kuri’u 2,476, yayin da Mkhize ya samu kuri’u 1,897.  (Saminu Alhassan)