logo

HAUSA

Mamakon ruwan sama ya yi sanadiyyar rasuwar mutane 16 a birnin Johannesburg

2022-12-18 15:57:13 CMG Hausa

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi ta samu tun cikin makwanni 2, ya haifar da lalacewar gidaje da hanyoyi, lamarin da kuma ya yi sandiyyar rasuwar mutane 16, a birnin Johannesburg na Afirka ta kudu.

Yayin zantawa da manema labarai game da hakan a jiya Asabar, mai rike da mukamin magajin garin birnin mafi girma a Afirka ta kudu, uwargida Mpho Phalatse, ta ce sakamakon ayyukan ceto da ‘yan sanda ke gudanarwa, an yi nasarar ceto rayukan mutane 148.

Baya ga gidaje da hanyoyi, ruwan saman kamar da bakin kwarya, ya kuma lalata muhimman ababen more rayuwar jama’a, kamar fitilun ba da hannu dake tituna, da tashoshin samar da lantarki da bututai, tare da hallaka dabbobi da tsirrai masu tarin yawa. (Saminu Alhassan)