logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya za ta samar da wutan lantarki mai karfin Megawatt 30 ta amfani da iska da hasken rana a jihar Sokoto

2022-12-17 14:29:37 CMG Hausa

A ranar 15 ga wata ne ma’aikatar kimiya da fasaha da kirkire-kirkire ta tarayyar Najeriya ta kaddamar da taron karawa juna ilimi na tsawon kwanaki uku wanda ya mayar da hankali kan yadda za a samar da hasken wutan lartarki mai karfin Megawatt 30 a kananan hukumomi biyu dake jihar Sokoto a arewa masu yammacin Najeriya.

An dai gudanar da taron ne a Jami`ar Usman Danfodio dake Sokoto, kananan hukumomin Shagari da Bodinga ne za su amfana da wanann shirin.

Yunkurin samar da karin wutar lantarkin na da alaka da matakin da gwmanatin shugaba Muhammadu Buhari ke dauka na samar da karin megawatt dubu 30 nan da shekara ta 2030.

Gwamnatin Najeriya da sashen binciken makamashi na jami`ar Usman Danfodio dake Sakkwato ke kokarin samar da megawatt 30 na wutan lantarki a jihar Sakkwato ta amfani da makamashi mai tsafta wanda ba ya gurbata yanayi kamar amfani da Zafi da hasken Rana da Iska da karfin Ruwa da ake kira Renewable Energy.

Sanata Adeleke Olorun-nimbe, ministan ma`aikatar kimiya da fasaha da ma kere-kere na tarayyar Najeriya shi ne ya kaddamar da taron, inda yake cewa,“Wannan taron masu ruwa da tsaki da aka shirya na kwanaki uku a kan harkokin makamashi na da manufar bayar da dama a tattauna tare da bayar da shawarwari a kan yadda Najeriya za ta zakulo makamashin da take da shi ta kuma yi amfani da shi dan ciyar da kasar gaba, kuma ba abun mamaki ba ne da aka zakulo jihar Sokoto domin kaddamar da wannan aikin gwaji na samar da makamashi a Najeriya domin dukkanin bayanai da rahottannin da aka tattara sun nuna cewa jihar Sokoto na da iska da hasken rana da kuma ruwan da za su iya samar da makamashi, don haka yana da matukar muhimmanci a ce kasar Najeriya za ta ci gaba da tatso wadanan makamashin dake akwai domin ci gaba da inganta makamashin da take da shi  da magance matsalar wutar lantarki da take fama da su.”

Shi ma da yake karin haske a game da alfanun shirin, Farfesa Sani Sagir masani a kan harkar makamashi a tarayyar Najeriya ya ce,“Wannan yunkuri ya zo a kan lokacin da ya kamata, abin da ake son cimmawa shi ne kara inganta abubuwan da jihar ta Sakkawato ke da su ta fuskar makamashi musamman hanyar samar da wuta na asali wato ta amfani da ruwan madatsar Kayinji, samar da megawatt 30 na hasken wuta ga al’umomin wannan jiha zai rage nauyin da aka dorawa tsohuwar hanyar da take baiwa yankin wuta.”

Najeriya dai na daya daga cikin kasashen duniya da suke fama da matsalar sauyin yanayi, inda ko a taron da ya gudana a kasar Masar wanda ake kira da COP27 an jiyo shugaban kasa Muhammadu Buhari na korafi a kan yadda ambaliyar ruwa ya daidaita ’yan Najeriya inda ya ce a kalla mutum miliyan 1.4 sun rasa muhallan su saboda matsalar ambaliyar ruwa da ta shafi jahohi 34 daga cikin jihohi 36. (Garba Abdullahi Bagwai)