Wadanne sabbin damammaki ne Sin za ta samar ga tattalin arzikin duniya?
2022-12-17 19:28:16 CMG Hausa
Daga ranar 15 zuwa 16 ga watan Disamba, an gudanar da babban taron kolin tattalin arzikin kasar Sin na shekara shekara a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Taron ya takaita ayyukan tattalin arziki na bana, inda aka yi nazari kan halin da ake ciki a fannin tattalin arziki, da tsara ayyukan raya tattalin arziki a shekarar 2023. Kasashen waje sun damu musamman kan yadda tattalin arzikin kasar Sin zai kasance a shekarar 2023.
Taron ya jaddada cewa, "shekarar 2023 dake tafe, ya kamata mu nace kan ka'idar kwanciyar hankali da ci gaba a cikin kwanciyar hankali", "samar da ci gaba da inganta ayyukan raya tattalin arziki, da samun ci gaba mai inganci, da ci gaba mai yawa".
Wadannan kalamai, sun ba da jagora ga ayyukan raya tattalin arzikin kasar Sin a shekarar dake tafe, kuma wannan shi ma albishiri ne ga duniya. (Ibrahim)