logo

HAUSA

Ambaliyar ruwa ta halaka mutane dubu 1 da 400 a yankin yammaci da tsakiyar Afirka

2022-12-17 15:36:01 CMG Hausa

Hukumar kula da ayyukan jin kai ta MDD (OCHA) ta bayyana cewa, ruwan sama kamar da bakin kwarya da ambaliyar ruwa a sassan yammaci da tsakiyar Afirka, sun yi sanadiyar mutuwar mutane dubu 1 da 400 tare da raba wasu miliyan 2.9 da muhallansu.

Ofishin OCHA ya bayyana cewa, ambaliyar ruwa mafi muni da ba a taba ganinta ba a cikin shekaru da dama, ta yi sanadiyar rayukan mutane miliyan 8.2, da dabbobinsu da dukiyoyinsu da filayen noma a kasashe 20 na yankin. Ofishin ya ce ci gaba da ambaliyar, ta lalata gidaje sama da dubu 513

OCHA ya kara da cewa, yankunan tsakiyar Afirka da dama tuni suke fama da matsalar karancin abinci, da rashin abinci mai gina jiki, da rashin kwanciyar hankali, da tashe-tashen hankula. Hukumomin kasa da na kananan hukumomi ne ke jagorantar ayyukan kai dauki, tare da tallafin kungiyoyin agaji. (Ibrahim)