logo

HAUSA

Kasar Sin ta daidaita manufarta ta kandagarkin yaduwar cutar COVID-19 bisa la’akari da yanayin da kasar ke ciki

2022-12-16 10:46:15 CMG Hausa

Kasar Sin ta riga ta kwashe shekaru 3 tana kokarin daukar matakan kandagarkin yaduwar cutar COVID-19, da suka hada da gudanar da gwaji ga mutane, da killace wadanda suka kamu da cutar, da sa ido kan yanayin lafiyar jikin mutanen da ke son yin bulaguro, da dai sauransu. Sai dai a kwanakin baya, gwamnatin kasar ta sanar da daidaita matakan, da sassauta manufar killacewa. (Bello Wang)