logo

HAUSA

Wang Yi ya gabatar da rubutaccen jawabi a gun taron ministoci na G77 da kasar Sin

2022-12-16 11:28:19 CMG Hausa

Mamban majalisar gudanarwar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya ba da jawabi a rubuce, a gun taron ministocin kungiyar kasashe masu tasowa ta G77 da kasar Sin da aka shirya jiya Alhamis.

Cikin jawabinsa, Wang Yi ya gabatar da wasu shawarwari da suka hada da, na farko, sanya neman bunkasuwa a kan gaba cikin hadin gwiwar kasa da kasa. Na biyu, inganta farfadowar tattalin arziki bisa daidaito da dorewa. Na uku shi ne, inganta gina tsarin tattalin arzikin duniya mai adalci. Na hudu, hada karfi da karfe daga kasa da kasa wajen tafiya da zamani.

Wang Yi ya jaddada cewa, Sin za ta gabatar da damarmakin da za su taimakawa ci gaban kasa da kasa, da kara bayar da karfinta ga hadin gwiwa da ci gaban duniya, da gabatar da manufofinta don goyon bayan kasashe masu tasowa. Haka kuma, Sin za ta ci gaba da kasancewa aminiya ta kwarai kuma madogara ga kasashe masu tasowa, kuma mai goyon bayan kungiyar G77, tare da himmatuwa wajen bunkasuwa da farfadowa tare, da samar da kyakkyawar makoma ga zamantakewar bil’adam. (Safiyah Ma)