logo

HAUSA

Mataimakin firaministan kasar Sin ya bayyana imaninsa game da kyautatuwar yanayin tattalin arzikin kasar a badi

2022-12-16 12:40:23 CMG Hausa

A ranar 15 ga wata, mataimakin firaministan kasar Sin mista Liu He ya gabatar da jawabi a rubuce, a yayin shawarwari tsakanin jagororin masana’antu da na ‘yan kasuwa da ma tsoffin manyan jami’ai na Sin da kungiyar tarayyar Turai karo na biyar, inda ya jaddada cewa, hadin gwiwar ciniki da zuba jari ya kasance alaka ta kut da kut a tsakanin Sin da Turai, kuma kasar Sin na fatan ganin fadada hadin gwiwar sassan biyu ta fannonin tattalin arziki da ciniki da kiyaye muhalli da hada-hadar kudi da kimiyya da fasaha da dai sauransu, kuma su hada kai wajen kiyaye tsarin cinikayyar bangarori da dama da ke da kungiyar WTO a matsayin jigonsa.

Mista Liu He ya kuma bayyana imaninsa game da kyautatuwar yanayin tattalin arzikin kasar Sin a shekara mai zuwa. Ya ce, sana’o’in da suka shafi samarwa da dillancin gidaje sun kasance ginshikin tattalin arzikin kasar, kuma an riga an dauki wasu matakai don daidaita matsalolin da ka iya haddasa dakushewar wannan sashe, tare da yin la’akari da sabbin matakan da za a dauka, a wani kokari na kyautata sana’o’in da ma karfafa imanin da ake da shi game da kasuwar gidaje. Biranen kasar Sin za su ci gaba da bunkasa da sauri, kuma hakan zai samar da tallafi ga bunkasuwar sana’o’in da suka shafi gidaje yadda ya kamata.(Lubabatu)