logo

HAUSA

Al`ummar Kauyen Danca dake karamar hukumar Tangaza a jihar Sokoto sun koka kan karuwar hare-haren ’yan bindiga

2022-12-15 14:11:47 CRI

Al'ummar kauyen Danca, dake gundumar Salewa a karamar hukumar mulkin Tangaza dake Sakkwato a arewa maso yammacin Nijeria na ci gaba da kokawa a kan hare-haren ganin dama da ’yan bindiga ke kai musu ba dare ba rana.

Wannan na zuwa ne bayan harin  da ’yan bindigar suka kaiwa kauyen a marecen ranar Litinin inda suka kashe mutum 6 tare da cinnawa kauyen wuta.

Wakilin mu dake tarayyar Najeriya Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Baya ga kauyen na Danca dake Tangaza, yanzu haka garuruwa da dama ne ke fuskantar hare-haren ’yan bindiga inda suke  ci gaba da garkuwa da jama'a domin neman kudin fansa da ma sanya haraji ga al'ummomi muddin suna son zaman lafiya.

Bayanai daga kauyen na Dancan na nuni da cewa maharan sun yiwo gayya ne sabo da a baya sun sha yunkurin zuwa kauyen amma jama’a na fatattakar su.

Wani mazaunin kauyen da ya bukaci a boye sunan sa ya shaida min ta wayar tarho cewa yanzu haka suna karbar ta’aziyyar wadanda suka mutu.

“Da suka shigo garin mutum 5 suka harbe sai suka kore shanu da rakuma da tumakai. Wasu a cikin maharan kuma suka tsaya, inda suka cinnawa kauyen wuta.

“Yanzu haka hankalin mu gaba daya a tashe yake, wata mace ma konewa ta yi bayan an cinna wuta a dakin ta.

A hali da ake cikin mutane na ci gaba da shigowa suna yi mana gaisuwa kamar shugaban karamar hukumar Tangaza da DPO duk sun zo har jami’an soji ma sun zo mana gaisuwar wadanda suka rasu amma dai ba mu ji dadi ba a lokacin da muka nemi daukin jami’an soja ranar Litinin amma ba su zo ba sai ranar Talata da rana.”

Rahotannin daga yankin na nuni da cewa tuni jami`an tsaro suka dauki matakan kare kauyukan da ma kamo maharan domin su fuskanci shari’a.

Karamar hukumar yankin Tangaza dai na daga cikin yankunan dake fuskantar matsalolin ’yan bindiga domin ko a ranar 17 ga watan Satumbar 2020 ’yan bindigar sun kai hari gidan MADI hedikwatar karamar hukumar Tangaza inda suka kashe DPO da wani sefeton ’yan sanda.

A wata mai kama da wannan kuma ’yan bindiga a gabashin Sokoto sun sace wasu mutum 6 a kauyen Dan Kwari dake karamar hukumar Sabon Birni, rahotanni daga yanki na nuni da cewa ’yan bindigar sun bukaci da a fara biyan su Naira miliyan 2.5 a matsayin haraji kafin daga bisani a yi maganar kudin fansar mutum 6 dake hannun su. (Garba Abdullahi Bagwai)