Xi Jinping ya gabatar da rubutaccen jawabi ga taron kolin ’yan kasuwa na Sin da Latin Amurka
2022-12-15 11:27:07 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da rubutaccen jawabi ga mahalarta bikin bude taron kolin ’yan kasuwa na Sin da Latin Amurka a jiya Laraba, wanda a cikinsa ya bayyana cewa, Sin za ta tsaya tsayin daka kan manufar bude kofa ga kasashen waje, da bin tsarin bude kofa mai cike da moriyar juna da samun nasara tare, da kuma tsayawa tsayin daka kan daidaitacciyar hanyar dunkulewar tattalin arzikin duniya baki daya.
Kaza lika Sin za ta samar da sabuwar dama ga duniya bisa sabon ci gaban ta, da inganta gina tattalin arziki budadde ga kowa, ta yadda hakan zai kawo alheri ga jama’ar kasashen daban daban, ciki har da na Latin Amurka da kasashen Caribbean.
Shugaban kasar Ecuador Guillermo Lasso, ya halarci taron kolin na ’yan kasuwar Sin da Latin Amurka, ya kuma gabatar da jawabi. (Safiyah Ma)