logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Sauya Matakan Yaki Da Annobar COVID-19 Bisa Yanayin Da Take Ciki

2022-12-15 11:17:18 CMG HAUSA

Kwanan baya, gwamnatin kasar Sin ta kyautata matakan dakile, da kandagarkin annobar cutar numfashi ta COVID-19, a kokarin rika yaki da annobar ta hanyar kimiyya yadda ya kamata, da rubanya kokarin kiyaye lafiyar al’umma da rayukansu, da rage illolin da yaduwar annobar ke haifarwa ga ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasa gwargwadon karfinta. Yanzu haka al’ummar Sin suna farfado da ayyuka da zaman rayuwar su yadda ya kamata.

A farkon barkewar annobar, Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da gwamnatin kasar sun jaddada cewa, tilas ne a mayar da rayukan jama’a da lafiyarsu a gaba da komai. Yawan masu fama da annobar bisa jimillar yawan jama’ar kasa, da kuma yawan wadanda suka mutu sakamakon kamuwa da annobar a kasar Sin, dukkansu su ne mafi kankanta idan an kwatanta da na sauran manyan kasashen duniya.

Sakamakon kyawawan matakan yaki da annobar, da ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar, ya sa saurin karuwar tattalin arzikin kasar Sin ya bunkasa da kaso 8.1 a shekarar 2021, adadin da ya fi na sauran muhimman rukunonin tattalin arzikin duniya yawa. Haka kuma, kasar Sin tana ba da taimako wajen yaki da annobar a duniya, gwargwadon karfinta.

A halin yanzu ba a ga bayan annobar ba, kuma ana ci gaba da fama da ita. Kasar Sin ta kyautata matakan yaki da annobar, bisa yanayin da ake ciki, kuma bisa ka’idojin mayar da jama’a a gaban komai, da kuma yaki da annobar ta hanyar kimiyya. (Tasallah Yuan)