logo

HAUSA

Matshidiso Moeti ta bukaci a kara zuba jari a fannin kiwon lafiyar Afirka

2022-12-15 16:13:26 CMG HAUSA

 

Daraktar hukumar lafiya ta duniya WHO shiyyar Afirka Matshidiso Moeti, ta yi kira da a kara zuba jari domin karfafa tsarin kiwon lafiya mai juriya.

Jami’ar ta WHO ta yi kiran ne cikin jawabinta na bude taron kasa da kasa karo na 2, game da tsarin kiwon lafiya a nahiyar Afirka ko “CPHIA 2022”, wanda aka bude a ranar Talata, a birnin Kigali, fadar mulkin kasar Rwanda.

Matshidiso Moeti ta ce anbonar COVID-19 ta kara fito da muhimmancin zuba jari a fannin kiwon lafiya, don haka ana bukatar managarcin tsari da zai share fagen aiwatar da matakan gaggawa, yayin da ake tabbatar da gudanar da muhimman hidimomin kiwon lafiya a nahiyar.

Jami’ar ta kara da cewa, matakai managarta, a matakin kasa, da shirin ko ta kwana tsakanin tawagogin lafiya, na iya taimakawa wajen cimma nasarorin da ake fata.

Kaza lika, Moeti ta ce duk da kasancewar ana gudanar da ayyukan bai daya, da yawa daga wasu kasashen nahiyar ba su kai ga cimma nasarorin kiwon lafiya da aka tsara kammalawa nan zuwa shekarar 2030 ba.

Ta ce shiyyar Afirka, na farin ciki game da ci gaban da aka samu a fannin kiwon lafiya, duba da cewa, kididdiga ta nuna yadda muhimman hidimomin kiwon lafiya a nahiyar suka karu, daga kaso 39 bisa dari a shekarar 2010 zuwa kaso 51 bisa dari a shekarar 2022.

Taron CPHIA na 2022, wanda ke gudana tsakanin ranakun Talata zuwa Alhamis din nan, ya maida hankali ne ga zakulo hanyoyin ingiza dabarun shawo kan muhimman kalubalen lafiya a Afirka, da samar da tsarin kiwon lafiya mai juriya.

Taron na gudana ne karkashin jagorancin cibiyar kandagarki da yaki da cututtuka ta Afirka ko “Africa CDC”, da hadin gwiwar gwamnatin Rwanda. Kuma ya hallara ministocin lafiya daga kasashen Afirka, da masana kimiyya, da masu bincike daga sassa daban daban. (Saminu Alhassan)