Sin: Tattalin arzikin al’umma na watan Nuwamba ya ci gaba da farfadowa
2022-12-15 12:16:08 CMG Hausa
Bisa kididdigar da hukumar kididdigar kasar Sin ta fitar a yau Alhamis, a watan Nuwamba, jimilar shige da ficen hajoji a kasar Sin sun karu da kashi 0.1% bisa makamancin lokaci na bara, kana karin hajojin da kamfanonin kasar ke sarrafawa a cikin kasar sun karu da kashi 2.2% bisa makamancin lokaci na bara.
Kaza lika tsakanin watan Janairu zuwa watan Nuwamba, jimilar shige da ficen hajoji a kasar Sin ta karu da kashi 8.6%, bisa makamancin lokaci na bara, kuma karin hajojin da kamfanonin kasar ke sarrafawa a cikin kasar sun karu da kashi 3.8% bisa makamancin lokaci na bara. (Safiyah Ma)