Waiwaye Game Da Yadda Kasar Sin Ta Tallafawa Duniya a Fanin Yaki Da Annobar Covid-19
2022-12-15 19:11:29 CMG HAUSA
Daga Saminu Hassan
Tun bayan barkewar annobar COVID-19, kasashen duniya sun dukafa wajen ganin bayan cutar, ta hanyar daukar matakai daban daban a lokuta mabanbanta, kuma matakin samar da alluran rigakafi masu inganci na sahun gaba a wannan muhi
mmin aiki.
Cikin kusan shekaru uku da suka gabata, kasar Sin ta yi rawar gani a fannin bincike da samar da rigakafin COVID-19, inda ta sauke nauyin dake wuyanta ta fuskar samar da rigakafi mai inganci ga al’ummun duniya baki daya.
Cikin shekarar 2020, masu binciken kimiyya na kasar Sin sun kirkiro tare da gwada nau’o’in rigakafin wannan annoba daban daban, inda ya zuwa watan Mayun shekarar 2021 da ta gabata, hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO, ta sanya rigakafin Sinopharm cikin jerin rigakafin COVID-19 da aka amince a yi amfani da su a mataki na gaggawa. Rigakafin da ya zama na farko samfurin kasar Sin da WHO ta amince da shi, kuma na 6 a duniya da ya samu amincewar hukumar.
Daga bisani, kamfanin Sinovac ya sake fitar da karin rigakafin cutar ta COVID-19, wanda shi ma ya samu amincewar hukumar WHO domin amfani da shi a matakin gaggawa.
Idan an kwatanta da wasu nau’o’in rigakafin cutar COVID-19 na kamfanonin Moderna da Pfizer, samfurin rigakafin kasar Sin na da fifito, kasancewar za a iya daukar sa daga wuri zuwa wuri cikin na’urorin sanyaya abubuwa na amfanin yau da kullum, ba tare da sun lalace ba. Hakan na nufin rigakafin na Sin sun dace da yanayi irin na kasashe masu tasowa, wadanda ke da karancin wuraren adana rigakafi dake da bukatar wuraren ajiya masu sanyin gaske.
A daya bangaren kuma, tun bayan da kasar Sin ta shiga shirin samar da daidaito wajen rarraba rigakafin annobar COVID-19 wato shirin “COVAX” a watan Oktoban shekarar 2020, kasar ta ci gaba da mika kyautar rigakafin cutar ga sassa daban daban na duniya. A watan Agustan shekarar bara, Sin ta alkawarta ba da tallafin rigakafin COVID-19, wanda darajarsa ta kai dalar Amurka biliyan biyu ga kasashen duniya daban daban, tare da karin tallafin dala miliyan 100 ga shirin na COVAX.
Ya zuwa watan Mayun shekarar 2022, Sin ta samar da tallafin kayayyakin yaki da annobar ga kasashe 153, da hukumomin kasa da kasa masu nasaba da wannan aiki har 15.
Kasar Sin ta bayar da agajin rigakafin COVID-19 guda biliyan 2.2 ga kasashe daban daban. Kaza lika ta tura tawagogin kiwon lafiya zuwa kasashe 34, ta kuma rarraba kwarewar wannan muhimmin aiki na yakin da cutar tare da kasashen duniya sama da 180, da ma wasu hukumomin kasa da kasa, matakan da dukkaninsu suka yi matukar samun yabo daga daukacin sassan duniya, musamman ma kasashe masu tasowa wadanda su ne suka fi cin gajiya daga wadannan tallafi na Sin.