Gwamnatin tsakiya ta goyi bayan HK game da kare martabar kasa
2022-12-14 21:02:25 CMG Hausa
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta bayyana goyon bayanta ga gwamnatin yankin musamman na Hong Kong, wajen daukaka darajar taken kasar.
Goyon bayan gwamnatin tsakiya, na zuwa ne bayan da aka bayar da rahoton cewa, shafin matanbayi ba ya bata wato Google, ya ki sanya taken kasar Sin, a saman filin neman sakamakon kalmomin "Hong Kong" da "taken kasa" kamar yadda gwamnatin yankin musamman na Hong Kong ta bukata. (Ibrahim)