Ruwan sama kamar da bakin kwarya a babban birnin Congo (Kinshasa) ya haddasa mutuwar mutane a kalla 141
2022-12-14 14:38:42 CMG Hausa
Tun daga daren ranar Litinin zuwa safiyar jiya Talata, an samu mamakon ruwan sama a birnin Kinshasa, fadar mulkin kasar Congo (Kinshasa), lamarin da ya haifar da ambaliya da zaftarewar kasa a sassan birnin, wanda hakan ya haddasa mutuwar mutane a kalla 141.
Ma’aikatar kiwon lafiya ta lardin Kinshasa ta sanar a daren jiya Talata cewa, yawancin mutanen da suka rasu suna zaune ne a wajen birnin na Kinshasa. Ambaliyar ruwan da zaftarewar kasa, sun lalata gidaje masu yawa, kuma wasu hanyoyin birnin sun yi ramuka.
Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta sanar a daren jiyan cewa, shugaban kasar Felix Tshisekedi, ya ba da umurnin gudanar da makokin wadanda suka rasu a dukkanin kasar tun daga yau Laraba zuwa ranar Juma’a 16 ga wata. (Safiyah Ma)