logo

HAUSA

Afirka ta Kudu za ta zama shugabar karba-karba ta kungiyar BRICS a shekara mai zuwa

2022-12-13 11:25:56 CMG Hausa

A jiya ne ministar hulda da kasa da kasa da hadin gwiwa ta kasar Afirka ta Kudu Naledi Pandol, ta kira taron manema labarai, inda ta gabatar da wasu nasarorin da kasarta ta cimma a manufofin ketare, da muhimman batutuwa da kalubalolin da ta fama da su a shekarar 2022, tare da gabatar da wasu muhimman abubuwan da kasar sanya su a gaba kuma za ta yi a shekarar 2023. Ta bayyana cewa, Afirka ta Kudu za ta karbi shugabancin karba-karba na kungiyar BRICS a shekara mai zuwa.

Pandor ta bayyana cewa, babban makasudin kasar na shiga kungiyar BRICS, shi ne inganta ci gabanta nan gaba, da karfafa huldar cikin gida da hadin gwiwar moriyar juna tsakanin kasashen BRICS. Ta ce tana ba da gudummawa kai tsaye da kuma a fakaice ga abubuwa masu kyau ga kasar, da Afirka da kuma duniya baki daya, ta hanyar hadin gwiwa da manyan masu ruwa da tsaki kan batutuwan da suka shafi harkokin tafiyar da duniya da gyare-gyare da ci gabanta. (Safiyah Ma)