Jakadan Nijar a China: Kasar Sin ta bayar da gudummawa sosai wajen samar da ci gaba ga Jamhuriyar Nijar
2022-12-13 15:42:23 CMG Hausa
A ‘yan shekarun nan, ana kara cimma nasarori wajen habaka hadin-gwiwa tsakanin kasar Sin da Jamhuriyar Nijar, ciki har da wasu muhimman ababen more rayuwar al’umma da kamfanonin kasar Sin suka gina a Nijar, wadanda suka zama tamkar “gadojin sada zumunta” tsakanin kasashen biyu. Wadannan muhimman ayyukan sun hada da, babbar gadar Janal Seyni Kountche, da tashar samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa ta Kandadji, da makamantansu.
Kwanan nan, jakadan Jamhuriyar Nijar dake kasar Sin Seyni Garba, ya zanta da manema labarai, inda a cewarsa, al’ummar kasarsa sun yaba matuka da muhimman ayyukan da kasar Sin ta gina a Nijar, kana, akwai kasashe masu tasowa da dama da suka ci gajiya daga hikimomin kasar Sin a fannin raya tattalin arziki.
Seyni Garba ya fara zama jakadan Jamhuriyar Nijar a watan Yulin shekarar da muke ciki, yana mai cewa:
“Wannan ne karo na farko da na zo kasar Sin, inda na riga na fahimci cewa, Sin babbar kasa ce mai ci gaba, kuma ana samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a ko’ina.”
Duk da cewa bai dade a kasar Sin ba, amma jakada Seyni Garba ya riga ya ziyarci sassa da dama a kasar, ciki har da Beijing, da Xinjiang, da Guangxi da sauransu, kuma yadda kasar Sin ta samu ci gaba ya burge shi kwarai da gaske. Jakadan ya ce, ba za’a iya raba dalilin ci gaban kasar Sin, da jagoranci na gari na jam’iyyar kwaminis mai mulkin kasar ba, wadda ita ce jam’iyyar dake bin akidar Markisanci mafi girma a duniya. Jakadan ya ce, jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa a fannin jagorantar kasar wajen samun ci gaban tattalin arziki da rayuwar al’umma.
Game da babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis karo na 20 da aka yi a watan Oktobar bana a Beijing, jakada Seyni Garba ya ce, wani babban al’amari ne ga kasar Sin, da ma duk duniya baki daya. Ba samar da alfanu ga jama’ar kasar Sin kawai jam’iyyar kwaminis take yi ba, har ma tana kokarin bayar da gudummawa ga ci gaban harkokin jama’ar duk duniya.
Kasar Sin mai saurin ci gaba, na kawo damammaki ga Jamhuriyar Nijar. Musamman ayyukan hadin-gwiwar da suka yi, sun amfani al’ummomin kasashen biyu. Alal misali, a kogin Neja, akwai wata babbar gadar zamani da ake kira Janal Seyni Kountche, wadda ta hade yankunan Goudel da Lamorde dake Yamai, babban birnin Nijar. Gwamnatin kasar Sin ce ta samar da tallafin gina gadar, wadda ake kiran ta da sunan “dutse mai daraja” a kogin Neja.
Jakada Seyni Garba ya ce:
“Sin babbar kasa ce ta farko da ta zuba jari a Jamhuriyar Nijar, kuma al’ummar kasarmu sun yaba sosai da muhimman ayyukan da kasar Sin ta gina, ciki har da babbar gada ta biyu da ta uku, wadanda suka ratsa kogin Neja dake birnin Yamai. Wadannan muhimman ababen more rayuwar al’umma, sun kawo sauki sosai ga harkokin surufi a Yamai.”
Tashar samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa ta Kandadji, shi ma wani kyakkyawan misali ne ga hadin-gwiwar kasar Sin da Jamhuriyar Nijar. Jakada Seyni Garba ya ce, tashar Kandadji, tashar samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa ce ta farko a kasar, inda yake cewa:
“Al’ummar Nijar suna sa ran alheri daga tashar Kandadji. Domin idan an kammala ta, za ta kara karfin samar da wutar lantarki a kasar. Har wa yau, za ta taimaka ga ci gaban ayyukan gonar mu, saboda za’a kyautata ingancin gonakin da fadin su ya kai hekta dubu 45.”
Baya ga shimfida hanyoyin mota da manyan gadoji, kasar Sin ta kuma nuna babban goyon-baya ga raya sana’ar hako albarkatun mai a Nijar. Matsalar rashin kwarewar sarrafa albarkatun man fetur, ta dade da ci wa Nijar tuwo a kwarya, har ma da kawo tsaiko ga ci gaban tattalin arziki da rayuwar dan Adam. Zuwan kamfanonin kasar Sin, ya sake baiwa al’ummar Nijar kwarin-gwiwar farfado da masana’antun man fetur. A shekara ta 2011, an kammala katafaren aikin gina filin hako man fetur na Agadem, wanda kamfanin kula da harkokin man fetur na kasar Sin mai suna CNPC ya bada taimakon ginawa, al’amarin da ya sa Nijar ta shiga jerin kasashe masu samar da man fetur da tace shi a duniya, kana, tana iya samar da isasshen man fetur daidai da bukatun kan ta. A shekara ta 2021, kamfanin kasar Sin ya fara shimfida bututun gurbataccen mai tsakanin Nijar da Benin, wanda idan an kammala aiki, Nijar za ta iya cimma burin fitar da gurbataccen mai zuwa kasashen waje, al’amarin da zai iya samar da babban ci gaba ga kasar.
Jakada Seyni Garba ya ce, duba da yadda kamfanonin kasar Sin suka bada tabbacin fasahohi, sana’ar sarrafa man fetur a Nijar ta samu bunkasa cikin saurin gaske a wadannan shekaru, haka kuma akwai sauran wasu kasashe masu tasowa da dama, wadanda suka ci gajiya daga bunkasar tattalin arziki da fasahohin kasar ta Sin.
Akwai dadadden zumunci tsakanin kasar Sin da Jamhuriyar Nijar, musamman lokacin da ake fuskantar matsaloli. A ranar 19 ga watan Maris din shekara ta 2020, an samu mutum na farko da ya kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a Nijar, amma kasar na fama da rashin isassun kayan yaki da annobar. A ranar 30 ga watan Afrilu, gwamnatin Nijar ta samu kashin farko na kayayyakin yaki da annobar da gwamnatin kasar Sin ta tallafa. Daga baya a ranar 10 ga watan Yuni, kashi na biyu na kayayyakin yaki da annobar da gwamnatin kasar Sin ta tallafa, suka isa birnin Yamai.
Seyni Garba ya bayyana cewa:
“Sin kasa ce ta farko da ta samar da kyautar alluran rigakafin cutar COVID-19 gami da kayayyakin yaki da cutar ga Jamhuriyar Nijar. Nijar ta gode mata kwarai da gaske, saboda irin wannan abun kirki da ta aikata.”
Jakada Seyni Garba ya kara da cewa, yaki da annobar COVID-19 kafada da kafada, wani bangare ne na hadin-gwiwar Sin da Nijar a harkar kiwon lafiya. A watan Agustar shekara ta 2016, an kammala aikin gina babban asibitin misali na Nijar, wanda ya kasance daya daga cikin asibitoci mafi girma a Nijar har ma a yammacin nahiyar Afirka, asibiti ne da kamfanin kasar Sin ya gina tare da hadin-gwiwar Nijar. Tun bayan da kasashen biyu suka rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin-gwiwar su a fannin kiwon lafiya a shekara ta 1976, kawo yanzu, kasar Sin ta shafe tsawon shekaru 46 tana aikewa da tawagar ma’aikatan lafiya zuwa Nijar, wadanda suka bada babban taimako wajen kula da marasa lafiya a kasar.
Tun daga gina muhimman ababen more rayuwar al’umma, har zuwa hadin-gwiwar harkokin kiwon lafiya, tun daga mu’amalar al’adu, har zuwa cudanyar tattalin arziki da kasuwanci, hadin-gwiwar kasar Sin da Jamhuriyar Nijar a bangarori daban-daban, na kawo babban alfanu ga al’ummar Nijar, wadanda suka zama tamkar “gadojin sada zumunta” tsakanin al’ummomin kasashen biyu. Kamar yadda jakada Seyni Garba ya ce, hadin-gwiwar kasashen biyu, abun misali ne, kana, a matsayin su na aminan juna, al’ummar Sin da Nijar za su kara samun fahimtar juna da hadin-gwiwa tsakanin su. (Murtala Zhang)