Manyan jami'an Sin da Amurka sun yi shawarwari a lardin Hebei na kasar Sin
2022-12-13 13:31:53 CMG Hausa
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana jiya Litinin cewa, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Xie Feng, ya yi shawarwari da mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka mai kula da harkokin gabashin Asiya da tekun Pasifik Daniel Kritenbrink, da babbar darekta mai kula da harkokin kasar Sin a majalisar tsaron Amurka Laura Rosenberger, ranar 11 da 12 ga watan Disamba a lardin Hebei dake arewacin kasar Sin.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yayin taron manema labarai na yau da kullum cewa, bangarorin biyu sun yi tattaunawa mai zurfi, kan yadda za a aiwatar da yarjejeniyar da shugabannin kasashen Sin da Amurka suka cimma a watan da ya gabata a birnin Bali na kasar Indonesia.
Wang ya ce, bangarorin biyu sun kuma tattauna kan ci gaba da tuntubar juna, kan ka'idojin Sin da Amurka, da dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata, kamar batun yankin Taiwan, da karfafa mu'amala a dukkan matakai, da hadin gwiwa a wasu fannoni.
Bugu da kari, sun yi musayar ra'ayoyi da dama kan batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya masu muhimmanci dake shafar muradunsu na bai daya, in ji kakakin, inda ya kara da cewa, bangarorin biyu sun amince cewa, tattaunawar ta gaskiya ce, mai zurfi da kuma inganci, kuma za su ci gaba da tuntubar juna.
Sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar na nuna cewa, ziyarar za ta share fagen ziyarar da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken zai kawo kasar Sin a farkon shekarar 2023. (Ibrahim Yaya)