logo

HAUSA

Ta yaya ake kare matasa da kananan yara daga kasa ganin abubuwa masu nisa?(B)

2022-12-12 13:05:18 CMG HAUSA

Masu karatu, a cikin shirinmu da ya gabata, na gabatar muku wasu shawarwari dangane da yadda ake kare matasa da kananan yara daga kasa ganin abubuwa masu nisa, alal misali, a kula da yanayin zama yayin da ake karatu ko rubutu, a kaurace wa barin idanu su gaji. Na kuma gabatar muku ka'ida mai saukin aikatawa, wato 20 da 20 da 20. Yayin da ake amfani da kayan laturoni na zamani, ya fi kyau a dan huta dakikoki 20 a kau da ido daga kayan cikin ko wadanne minti 20, a kalli abubuwan da ke da nisan kafa 20, kwatankwacin mita 6. Yau bari in ci gaba da ba ku karin shawarawri.

Ya kamata kananan yara da matasa su kara motsa jiki a wajen daki. Masana ilmin cututtukan idanu da suka fito daga kasar Jamus sun yi bayani da cewa, hanya mafi dacewa da za a bi wajen rigakafin gamuwa da matsalar kasa ganin abubuwa masu nisa, ita ce daukar isasshen lokaci na motsa jiki a wajen daki, alal misali, matasa da kananan yara sun dauki awoyi 2 suna motsa jiki a wajen daki a ko wace rana. Matasa da kananan yara su kan gamu da matsalar kasa ganin abubuwa masu nisa a lokacin da shekarunsu suka kai 8 zuwa 15 da haihuwa, amma hakika dai idanunsu suna girma har shekarunsu su kai 16 zuwa 18. Don haka kafin shekarunsu sun kai 16 zuwa 18 a duniya, hasken rana isasshe yana taimakawa wajen dakatar da gamuwa da matsalar kasa ganin abubuwa masu nisa. Baya ga haka kuma, masana daga kasar Koriya ta Kudu sun nuna cewa, tabbatar da motsa jiki isasshe a wajen daki a ko wace rana, da kasancewa a karkashin hasken rana don kara azama kan samun bitamin D a jiki, dukkansu suna taimakawa wajen yin rigakafin gamuwa da matsalar kasa ganin abubuwa masu nisa.

Haka zalika, a binciki idanu lokaci zuwa lokaci. Masanan daga Koriya ta Kudu sun bada shawarar cewa, ya fi kyau a binciki idanu a ko wane rabin shekara. Dangane da haka, madam Zhang Chuji, likita da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi karin bayani cewa, kamata ya yi iyaye su kai yaransu wajen likita don binciken idanunsu a ko wane rabin shekara ko kuma a ko wace sheakara. Kana kuma, ya kamata a hana kananan yara da matasa amfani da kayan laturoni na zamani awa 1 zuwa 2 kafin sun yi barci. (Tasallah Yuan)