logo

HAUSA

Taron kolin Sin da kasashen Larabawa zai ciyar da huldarsu gaba zuwa sabon mataki

2022-12-11 15:31:40 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da wani muhimmin jawabi a yayin taron kolin kasar Sin da kasashen Larabawa karo na farko a birnin Riyadh, fadar mulkin kasar Saudiyya a ranar 9 ga wata, inda ya jaddada cewa, ya dace a gada, da kuma habaka ruhin sada zumunta dake tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa, mai kunshe da cewa: “Taimakawa juna, da samun moriya tare, bisa tushen daidaito, da kuma yin hakuri ga juna”, tare kuma da gina kyakkyawar makomar Sin da kasashen Larabawa ta bai daya.

Ban da haka Xi, ya gabatar da ayyuka guda takwas, game da hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu. Bayan taron, kasar Sin da kasashen Larabawa sun fitar da “Sanarwar Riyadh, kan taron kolin kasar Sin da kasashen Larabawa karo na farko”, da sauran muhimman takardu, inda sassan biyu suka amince da gina kyakkyawar makomar Sin da kasashen Larabawa ta bai daya, a sabon zamanin da suke ciki. Ana iya cewa, wannan shi ne sakamakon siyasa mafi muhimmanci ne da aka samu yayin taron kolin.

Hakika, wannan taro shi ne karo na farko da sassan biyu suka kira, tun bayan kafuwar sabuwar kasar Sin a shekarar 1949. A halin yanzu duniyarmu tana fuskantar tangarda, don haka kasar Sin da kasashen Larabawa, sun cimma matsaya guda, kan batun game da kiyaye tsarin duniya, da manufar gudanar da harkokin kasa da kasa tsakanin bangarori daban daban bisa tushen dokar kasa da kasa, ta yadda za a kiyaye moriya, da hakki na kasashe masu tasowa. Kaza lika ana iya cewa, kirar wannan taron kolin a wannan lokaci yana da babbar ma’ana. (Jamila)