logo

HAUSA

An fitar da sanarwa kan yanayin siyasa a gabashin DRC

2022-12-11 15:53:59 CMG Hausa

Jiya Asabar 10 ga wata, shugaban kungiyar tarayyar Afirka wato AU na wannan zagaye, kuma shugaban kasar Senegal Macky Sall, da shugaban hukumar AU Moussa Faki Mahamat, sun fitar da hadaddiyar sanarwa, inda suka yi suka da babbar murya, kan kisan fararen hula a yankin gabashin kasar demokuradiyar Kongo, a ranar 29 ga watan Nuwamban da ya gabata.

Cikin sanarwar, kungiyar AU ta yi Allah wadai da kakkausar murya, bisa aikata wannan mummunan laifi, ta kuma bukaci a hukunta wadanda suka aika laifin bisa doka, kuma a kan lokaci.

Sanarwar ta kara da cewa, AU ta bukaci daukacin dakaru, da su ajiye makamai, kuma su halarci shawarwarin siyasa, domin wanzar da zaman lafiya, ba tare da gindaya ko wane irin sharadi ba. (Jamila)