logo

HAUSA

Hulda tsakanin Sin da kasashen yankin Gulf za ta samu sabon kuzari

2022-12-11 15:38:21 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci taron kolin kasar Sin da kungiyar hadin gwiwa tsakanin kasashen Larabawa dake yankin Gulf karo na farko a birnin Riyadh, fadar mulkin kasar Saudiyya a ranar 9 ga wata, inda ya gabatar da wani muhimmin jawabi. Wannan ne dai karo na farko da shugabannin kasar Sin, da shugabannin kasashen mambobin kungiyar suka gana kai tsaye, domin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakaninsu.

Yayin taron kolin, sassan biyu sun tsaida kuduri cewa, za su kafa, da kuma kara karfafa huldar abokantaka tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare, wanda hakan babban sakamako ne da suka samu yayin taron, saboda lamarin ya bude sabon shafin hadin gwiwar sassan biyu.

Kungiyar hadin gwiwa tsakanin kasashen Larabawa dake yankin Gulf, babbar kungiyar siyasa da tattalin arziki ce a yankin Gulf, wadda ke kumshe da kasashe mambobi guda shida, wato Saudiyya, da Qatar, da Kuwaiti, da Oman da kuma Bahrain. Hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen dake yankin na Gulf, ta fi hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da sauran kasashen dake yankin Gabas ta Tsakiya kyau, sakamakon amincewa da junansu a bangaren siyasa, da zumuncin dake tsakanin al’ummomin sassan biyu, musamman ma a cikin shekaru goma da suka gabata. Bugu da kari, hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu ya samu babban sakamako, har sun daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa da dama, bisa shawarar ziri daya da hanya daya.

Yanzu haka kasar Sin da kasashen Larabawa dake yankin Gulf, suna fuskantar kalubalen dake gaban dukkanin duniya, musamman ma wajen magance karancin abinci da makamashi, hakan ya sa ya dace su kara karfafa hadin gwiwa tsakaninsu, domin samun ci gaba tare. (Jamila)