logo

HAUSA

Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Algeria

2022-12-10 17:14:36 CMG Hausa

Jiya da dare ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Algeria Ayman Benabderrahmane a birnin Riyadh dake kasar Saudiyya.

A yayin ganawar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin tana goyon bayan kasar Algeria wajen tabbatar da ikon mulki, da ‘yancin kai, da cikakkun yankunan kasar, da kuma bin hanyar neman bunkasuwa da ta dace da yanayin kasar, kana tana adawa da tsoma baki daga sauran bangarorin waje kan harkokin cikin gidan kasar Algeria. 

Sin tana son ci gaba da yin hadin gwiwa tare da kasar Algeria a fannonin ayyukan more rayuwa, da makamashi, da hakar ma’adinai, da binciken sararin samaniya da sauransu bisa tsarin shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya”, da kuma sa kaimi ga karin kamfanonin Sin da su shiga aikin gina manyan ayyuka a kasar Algeria.

A nasa bangare, Benabderrahmane ya bayyana cewa, ya nuna godiya ga kasar Sin kan yadda take nuna goyon baya ga kasarsa, ciki har da samar da alluran rigakafin cutar COVID-19, matakin da ya kai ga hada alluran da kanta a kasar Algeria, kuma kasar Algeria ba ta manta da wannan karamci ba. Ya kara da cewa, kasar Algaria za ta ci gaba da nuna goyon baya ga ka’idar Sin daya tak a duniya, da rashin tsoma baki kan harkokin cikin gida na sauran kasashe, da kuma cimma moriyar daukacin dan Adam. Kasar Algeria tana fatan kara yin hadin gwiwa tare da kasar Sin a fannin ayyukan more rayuwa da sauransu don sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakaninta da Sin, da ma tsakanin Afirka da Sin zuwa wani sabon matsayi. (Zainab)